LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Disamba 2018
Yadda Za Mu Yi Wa’azi
Jerin tattaunawa game da yadda za mu sake ganin ’yan’uwanmu da suka mutu.
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Mai Tsananta wa Kiristoci Ya Zama Kirista Mai Kwazo
Idan ana nazarin Littafi Mai Tsarki da kai, amma ba ka yi baftisma ba tukuna, za ka bi misalin Shawulu ta wurin aikata abubuwan da kake koya?
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Barnaba da Bulus sun yi wa’azi a wurare da nesa
Duk da tsanantawa mai tsanani da Barnaba da Bulus suka fuskanta, sun ci gaba da taimaka wa mutane su zama Kiristoci.
RAYUWAR KIRISTA
Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Taimaka Ma Wadanda Suke So Su Zama Mabiyan Yesu
Ta yaya muke aiki tare da Jehobah a wa’azi?
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
An Dauki Mataki da Ya Yi Daidai da Kalmar Allah
Mene ne za mu koya daga yadda aka warware matsalar nan?
RAYUWAR KIRISTA
Mu Yabi Jehobah Ta Wurin Rera Waka da Farin Ciki
Wane amfani ne za mu samu daga rera wakokin Mulkin?
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ku Yi Koyi da Yadda Bulus Ya Yi Wa’azi da Kuma Koyarwa
Ta yaya za mu bi misalin manzo Bulus?
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ku Lura da Kanku, da Kuma Dukan Garken”
Dattawa suna kula da ciyar da kuma kāre tumakin Yesu. Kuma sun san cewa da jinin Yesu ne aka fanshi kowane tumakinsa.