RAYUWAR KIRISTA
Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Taimaka Ma Wadanda Suke So Su Zama Mabiyan Yesu
MUHIMMANCINSA: Jehobah yana taimaka ma “waɗanda suke da zuciya ta samun rai na har abada” su zo su bauta masa. (A. M 13:48, New World Translation; 1Ko 3:7) Muna wannan aikin tare da shi ta wajen mai da hankali ga waɗanda suke aikata abin da suke koya. (1Ko 9:26) Muna bukatar mu taimaka musu su fahimci cewa wajibi ne su yi baftisma idan suna son su sami ceto. (1Bi 3:21) Mu taimaka wa ɗalibanmu su zama mabiyan Yesu ta wajen koya musu yadda za su gyara rayuwarsu da yin wa’azi da kuma keɓe kansu ga Jehobah.—Mt 28:19, 20.
YADDA ZA MU CIM MA HAKAN:
-
Ku tuna wa ɗalibanku cewa ainihin dalilin da ya sa kuke nazari da su shi ne don su “san” Jehobah kuma su faranta masa rai.—Yoh 17:3
-
Ku taimaka musu su daina halayen banza da kuma tarayya da abokan banza
-
Ku riƙa ƙarfafa su sosai kafin su yi baftisma da kuma bayan sun yi hakan.—A. M 14:22
KU KALLI BIDIYON NAN JEHOBAH ALLAH ZAI TAIMAKE KA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
-
Mene ne zai iya sa mutum ya ji tsoron yin alkawarin bauta ma Jehobah kuma ya yi baftisma?
-
Ta yaya dattawa za su taimaka wa ɗaliban Littafi Mai Tsarki su sami ci gaba a ibadarsu?
-
Mene ne littafin Ishaya 41:10 ya koya mana game da Jehobah?
-
Waɗanne halaye ne za su taimaka mana mu bauta wa Jehobah da kyau duk da cewa mu ajizai ne?