Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

’Yan’uwa suna saurarar hukuncin da hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci ta yanke

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYYUKAN MANZANNI 15-16

An Dauki Mataki da Ya Yi Daidai da Kalmar Allah

An Dauki Mataki da Ya Yi Daidai da Kalmar Allah

Mene ne za mu koya daga yadda aka warware matsalar nan?

15:​1, 2—Mu kasance da sauƙin kai da kuma haƙuri. Maimakon Bulus da Barnaba su sasanta matsalar da kansu, sun nemi ja-gora daga ƙungiyar Jehobah.

15:​28, 29—Mu gaskata da ƙungiyar Jehobah. ’Yan’uwan da ke ikilisiyar sun gaskata cewa Jehobah zai yi amfani da ruhu mai tsarki da kuma Yesu Kristi don ya warware matsalar.

16:​4, 5—Mu yi biyayya. Ikilisiyoyin sun ci gaba da ƙaruwa kuma bangaskiyarsu ta ƙara yin ƙarfi domin sun bi umurnin hukumar da ke kula da ayyukansu a lokacin.