16-22 ga Disamba
RU’UYAR DA AKA YI WA YOHANNA 13-16
Waƙa ta 55 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Kada Ku Ji Tsoron Dabbobin Nan Masu Ban Tsoro”: (minti 10)
R. Yar 13:1, 2—Dodon nan mai siffar maciji ya ba wa dabbar da take da ƙahoni goma da kawuna bakwai iko (w12 6/15 8 sakin layi na 6)
R. Yar 13:11, 15—Dabbar da take da ƙahoni biyu ta ba wa dabba ta farko rai (mwbr19.12-HA an ɗauko daga re 194 sakin layi na 26; 195 sakin layi na 30-31)
R. Yar 13:16, 17—Kar mu bari a saka mana lambar dabbar (w09 2/15 4 sakin layi na 3)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
R. Yar 16:13, 14—Ta yaya za a tattara ƙasashe zuwa “yaƙi a babbar Ranar nan ta Allah Mai Iko Duka”? (w09 2/15 4 sakin layi na 6)
R. Yar 16:21—Wane saƙo ne za mu yi shelarsa kafin a halaka duniyar Shaiɗan? (w15 7/15 16 sakin layi na 9)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) R. Yar 16:1-16 (th darasi na 10)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Bidiyon Komawa Ziyara ta Farko: (minti 5) Ku kalli bidiyon kuma ku tattauna shi.
Komawa Ziyara ta Farko: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. (th darasi na 2)
Komawa Ziyara ta Farko: (minti 5 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Sai ka gabatar da kuma tattauna (kada ka kunna) bidiyon nan Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? (th darasi na 11)
RAYUWAR KIRISTA
Kada Ku Saka Hannu A Harkokin Duniya: (minti 15) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon nan Kasancewa da Aminci a Furuci da Halinmu. Sai ka yi tambayar nan, Ta yaya za mu ƙi saka baki a harkokin duniya? Bayan haka, sai ku kalli bidiyon nan Kasancewa da Aminci A Dukan Lokaci. Sai ka yi tambayar nan, Ta yaya za ka yi shiri don wani yanayin da zai iya gwada amincinka?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) bhs babi na 18 sakin layi na 12-22
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 131 da Addu’a