Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Yin La’akari da Yanayin Mutane

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Yin La’akari da Yanayin Mutane

MUHIMMANCIN YIN HAKAN: Shafaffu da kuma sauran tumaki suna gayyatar dukan mutane su zo su “karɓi ruwa mai ba da rai kyauta.” (R. Yar 22:17) Wannan ruwan yana wakiltar dukan tanadin da Jehobah yake yi wa mutane don ya cece su daga zunubi da kuma mutuwa. Don mu iya taimaka wa mutanen da suka fito daga ƙasashe dabam-dabam kuma suke da addini iri-iri, wajibi ne mu yi shelar “labari mai daɗi” a hanyar da za ta ratsa zuciyarsu.​—R. Yar 14:6.

YADDA ZA MU YI HAKAN:

  • Ka zaɓi batu da kuma nassin da za su ratsa zuciyar mutanen da suke yankinku. Kana iya bin ɗaya daga cikin shawarar da ake ba mu a kan yadda za mu riƙa yin wa’azi ko kuma wani batu da ka taɓa amfani da shi kuma mutane suka ji daɗinsa. Wane batu ne ko nassi mutanen yankinku suka fi jin daɗinsa? Akwai wani abu da ya faru da mutane suke magana a kai? Wane batu ne zai fi jan hankalin namiji ko tamace?

  • Ka gai da mutanen da ke yankinku yadda ake yi a al’adarsu.​2Ko 6:​3, 4

  • Ka san littattafanmu da kuma bidiyonmu na wa’azi sosai don ka iya amfani da su idan ka haɗu da wani da ke son saƙonmu

  • Ka sauƙar da littattafai da bidiyo daga dandalinmu a yaren mutanen da ke yankinku

  • Ka canja batun da kake tattaunawa bisa yanayin maigidan. (1Ko 9:​19-23) Alal misali, me za ka ce idan ka ji cewa an yi wa maigidan rasuwa?

KU KALLI BIDIYON SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wane batu ne mai shelan ya soma tattaunawa da maigidan?

  • Wace matsala ce maigidan yake fuskanta?

  • Wane nassi ne ya fi dacewa da yanayin nan kuma me ya sa?

  • Ta yaya kake canja yadda kake wa’azi don ka ratsa zuciyar mutanen da ke yankinku?