Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | RU’UYAR DA AKA YI WA YOHANNA 10-12

An Kashe “Shaidu Biyu” Kuma An Tashe Su

An Kashe “Shaidu Biyu” Kuma An Tashe Su

11:3-11

  • “Shaidun nan biyu”: Suna wakiltar ƙaramin rukunin shafaffun Kiristoci da suke ja-gora sa’ad da aka kafa Mulkin Allah a 1914

  • An kashe su: Bayan sun yi wa’azi na shekaru uku sanye da “rigunan makoki,” an “kashe su” sa’ad da aka saka su a fursuna kuma aka hana su wa’azi

  • An tashe su: Bayan kwanaki uku da rabi na alama, an tashe su sa’ad da aka sake su daga fursuna kuma suka ci gaba da yin ja-gora a wa’azi