RAYUWAR KIRISTA
Kasar Ta “Shanye Ruwan Kogin”
A zamanin dā, hukumomin gwamnati sun taimaka wa bayin Jehobah. (Ezr 6:1-12; Es 8:10-13) Ko a yanzu ma, muna ganin yadda “ƙasar,” wato wasu hukumomi da suke da kirki a zamanin nan suke shanye “ruwan kogin” ko kuma dakatar da tsanantawa da “dodon” nan wato Shaiɗan yake sa a yi wa mutanen Allah. (R. Yar 12:16) A wasu lokuta, Jehobah, “Allah na ceto” yakan sa hukumomi su taimaka wa mutanensa.—Za 68:20; K. Ma 21:1.
Me za ka yi idan aka saka ka a fursuna don imaninka? Ka tabbata cewa Jehobah yana gani kuma zai kula da kai. (Fa 39:21-23; Za 105:17-20) Ban da haka ma, Jehobah zai albarkace ka don bangaskiyarka kuma amincinka zai ƙarfafa ’yan’uwa a faɗin duniya.—Fib 1:12-14; R. Yar 2:10.
KU KALLI BIDIYON NAN AN SAKI ’YAN’UWA DAGA GIDAN YARI A KORIYA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Me ya sa an yi shekaru ana saka ’yan’uwanmu da yawa a fursuna a Koriya ta Kudu?
-
Wane mataki ne hukumomi suka ɗauka da ya sa aka sako ’yan’uwanmu tun lokacinsu bai yi ba?
-
Ta yaya za mu taimaka wa ’yan’uwanmu da suke fursuna domin imaninsu a faɗin duniya?
-
Ta yaya za mu yi amfani da ’yancin da muke da shi yanzu?
-
Waye yake taimaka mana mu yi nasara a shari’a da yawa da muke yi?