Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Ci Gaba da Amfani da Mujallu

Ku Ci Gaba da Amfani da Mujallu

Tun daga 2018, batu ɗaya kawai ake tattauna a kowace mujalla. Mujallun suna cikin littattafan da muke wa’azi da su. Don haka, za mu iya amfani da su a wa’azi. Za mu iya ɗauka kaɗan daga cikinsu yayin da muke tafiya ko za mu je sayayya. Ba a shirya mujallun don nazari da mutane ba, amma don su sa mutane marmarin koyan abubuwa game da Allah.

Bayan kun soma tattaunawa kuma ka karanta masa nassi, ka ambata wani batu a mujallar da mutumin zai so. Alal misali, idan mutumin magidanci ne ko kuma yana fama da baƙin ciki, kana iya ce masa: “Na taɓa karanta wani talifi game da wannan batu kuma na ji daɗinsa. Zan iya nuna maka?” Idan mutumin ya nuna yana son saƙon, ka ba shi ɗaya daga cikin mujallunmu ko kuma ka tura masa wanda yake dandalinmu, ko da wannan ne haɗuwarku ta fari. Ko da yake ba da mujallu ba shi ne ainihin makasudinmu ba, amma yin hakan zai taimaka mana mu san waɗanda suke marmarin koya game da Allah kuma su yi amfani da abin da suka koya.​—A. M 13:48.

2018

2019

2020

 

Wane batu ne mutanen yankinku suka fi so?