RAYUWAR KIRISTA
Za Ka Iya Cika Fom na Makarantar Masu Yada Bisharar Mulki?
Shin kana tsakanin shekaru 23 zuwa 65 kuma kana hidima ta cikakken lokaci? Kana da ƙoshin lafiya kuma za ka iya yin hidima a inda ake da bukatar masu shela? Idan ka amsa e ga waɗannan tambayoyin, ka taɓa yin tunanin cika fom na Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki? Tun daga lokacin da aka kammala aji na farko, dubban ma’aurata da ’yan’uwa maza da mata sun halarci makarantar. Amma an fi bukatar ’yan’uwa maza su halarci makarantar. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka zama da marmarin faranta masa rai kuma ka yi koyi da Ɗansa. (Za 40:8; Mt 20:28; Ibr 10:7) Don haka, ka yi tunanin hakkokin da kake da su kamar su hakkin kula da iyalinka ko aikinka ko kuma bashi da ake bin ka. Idan kana da ɗaya daga cikin waɗannan hakkokin, za ka iya daidai shi don ka iya cancanci zuwa makarantar?
A waɗanne hanyoyi da wurare ne waɗanda aka horar a makarantar za su iya yin hidima? An tura waɗanda suka sauke karatu a makarantar zuwa wuraren da ake wasu yaruka ko wuraren da ake wa’azi da amalanke na musamman. Wasu kuma daga baya sun zama masu taimaka wa mai kula da da’ira ko masu kula da da’ira ko kuma waɗanda suke wa’azi a ƙasashen waje. Yayin da kake tunanin yadda za ka faɗaɗa hidimarka ga Jehobah, ka kasance da ra’ayin annabi Ishaya wanda ya ce: “Ga ni nan, ka aike ni!”—Ish 6:8.
KU KALLI BIDIYON NAN MASU HIDIMA A ƘASASHEN WAJE SUNA WA’AZI DA ƘWAZO, SA’AN NAN KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Ta yaya ake zaɓan waɗanda suke hidima a ƙasashen waje?
-
Wane aiki mai kyau ne ’yan’uwa da suke wa’azi a ƙasashen waje suke yi?
-
Waɗanne albarku ne waɗanda suke wa’azi a ƙasashen waje suke samuwa?