RAYUWAR KIRISTA
Mu Nuna Kauna ga Jehobah ta Wajen Amincewa da Horonsa
Yankan zumunci na ƙare ikilisiya kuma horo ne ga waɗanda suka yi zunubi kuma suka ki tuba. (1Ko 5:6, 11) Muna nuna ƙauna idan muna goyon bayan horon Jehobah. Ta yaya hakan zai yiwu idan yankan zumuncin ya jawo baƙin ciki ga mutumin da iyalinsa da kuma dattawa?
Abin da ya fi muhimmanci shi ne, idan muka goyi bayan Jehobah muna nuna cewa muna ƙaunar sunansa da kuma tsari da ya kafa mana game da tsarki. (1Bi 1:14-16) Ban da haka ma, muna nuna ƙauna ga wanda aka yi masa yankan zumunci. Ko da yake horo na da zafi, “yakan haifar da adalci da salama.” (Ibr 12:5, 6, 11) Idan mun yi cuɗanya da wanda aka yi masa yankan zumunci ko kuma wanda ya bar ƙungiyar Jehobah, ba ma goyon bayan horon Jehobah ke nan. Ku tuna cewa Jehobah yana yi wa mutanensa horo “da shari’ar gaskiya.” (Irm 30:11) Fatanmu shi ne mutumin ya koma ga Ubanmu mai jinkai. Amma kafin mutumin ya komo, za mu ci gaba da goyon bayan yadda Jehobah yake ba da horo kuma mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ci gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da shi.—Ish 1:16-18; 55:7.
KU KALLI WASAN KWAIKWAYON NAN KU NUNA AMINCI DA DUKAN ZUCIYARKU, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Yaya iyaye suke ji sa’ad da ɗansu ya daina bauta wa Jehobah?
-
Ta yaya ikilisiya za ta iya taimaka ma iyayen?
-
Wane labarin Littafi Mai Tsarki ne ya koya mana cewa mu riƙa ƙaunar Jehobah fiye da membobin iyalinmu?
-
Ta yaya za mu nuna ma Jehobah ƙauna fiye da wani memban iyalinmu?