LITTAFIN FIRISTOCI 12-13
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH |Me Za Mu Koya Daga Dokar da Aka Bayar Game da Kuturta
13:4, 5, 45, 46, 52, 57
Me muka koya game da dokar da aka bayar game da kuturta wajen kāre dangantakarmu da Allah?
-
Jehobah ya nuna wa firistoci hanyoyin da za su bi don su gane mutanen da suke da cutar kuturta da sauri. Haka ma, dattawa ba sa ɓata lokaci wajen taimaka wa duk wanda yake bukatar gyara dangantakarsa da Jehobah.—Yaƙ 5:14, 15
-
An bukaci Isra’ilawa su ƙone duk wasu abubuwa da kuturta ta shafa don kada cutar ta yaɗu. Haka ma, ya kamata Kiristoci su yi watsi da wasu abubuwa da suke so idan har abubuwan za su sa su yi zunubi. (Mt 18:8, 9) Hakan ya ƙunshi wasu halaye da abokai da kuma nishaɗi
Ta yaya Kirista zai nuna cewa yana son Jehobah ya taimaka masa?