1- 7 ga Fabrairu
NEHEMIYA 1-4
Waƙa ta 126 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Nehemiya Ya So Bauta ta Gaskiya”: (minti 10)
[Ka sa bidiyon Gabatarwa ga Littafin Nehemiya.]
Ne 1:11–2:3—Nehemiya ya yi farin ciki da yadda aka faɗaɗa bauta ta gaskiya (w06 2/1 28 sakin layi na 7)
Ne 4:14—Nehemiya ya jimre da hamayya da aka yi wa bauta ta gaskiya ta wajen dogara ga Jehobah (w06 2/1 29 sakin layi na 3)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Ne 1:1; 2:1
—Me ya sa za mu ce ƙirgen “shekara ta ashirin” da aka ambata a Nehemiya 1:1 da 2:1 yana nuni ga lokaci ɗaya ne? (w06 2/1 27 sakin layi na 5) Ne 4:
17, 18 —Ta yaya mutum zai yi aikin gini da hannu ɗaya kawai? (w06 2/1 28 sakin layi na 1) Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ne 3:
1-14 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Ka Shirya Gabatarwa na Wannan Watan: (minti 15) Tattaunawa. Ka saka duka bidiyon, bayan haka, sai ka tattauna wasu abubuwa a ciki. Ka nanata yadda mai shelan ya yi wata tambaya ko kuma ya faɗi wani batun da za su tattauna sa’ad da ya koma ziyara. Ka ƙarfafa masu sauraro su rubuta nasu gabatarwar.
RAYUWAR KIRISTA
Waƙa ta 103
Ku Shirya Yin Majagaba na Ɗan Lokaci a Watan Maris ko Afrilu: (minti 15) Tattaunawa. Ka tattauna wasu muhimman darussa daga talifin nan “Yadda Za Ku Kasance da Farin Ciki a Lokacin Tuna da Mutuwar Yesu!” (km 2/14 2) Ka nanata muhimmancin yin shiri da wuri. (Mis 21:5) Ka gana da masu shela biyu da suka taɓa yin hidimar majagaba na ɗan lokaci. Waɗanne ƙalubale ne suka magance? Waɗanne sakamako masu kyau ne suka samu?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: ia babi na 8 sakin layi na 1-16 (minti 30)
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 135 da Addu’a