Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

22-28 ga Fabrairu

Nehemiya 12-13

22-28 ga Fabrairu
  • Waƙa ta 106 da Addu’a

  • Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

  • Darussan da Za Mu Koya Daga Littafin Nehemiya”: (minti 10)

    • Ne 13:4-9—Ku guji tarayya da mugaye (w13 8/15 4 sakin layi na 5-8)

    • Ne 13:15-21—Ka sa bautar Allah a kan gaba (w13 8/15 5-6 sakin layi na 13-15)

    • Ne 13:23-27—Ka kasance da halin Kirista (w13 8/15 6-7 sakin layi na 16-18)

  • Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)

    • Ne 12:31—Wane sakamako aka samu domin akwai rukunin mawaƙa guda biyu? (it-2 454 sakin layi na 1)

    • Ne 13:31b—Mene ne Nehemiya ya roƙi Jehobah ya yi masa? (w11 4/1 21 sakin layi na 3-5)

    • Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?

    • Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?

  • Karatun Littafi Mai Tsarki: Ne 12:1-26 (minti 4 ko ƙasa da hakan)

KA YI WA’AZI DA ƘWAZO

  • Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ku ba da takardar gayyata na Tunawa da Mutuwar Yesu ga wani da ya ɗan saurari saƙonmu.

  • Haɗuwa ta Fari: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Ku ba da takardar gayyata na Tunawa da Mutuwar Yesu da Hasumiyar Tsaro ga wani da ya saurari saƙonmu sosai. Ka yi wata tambaya ko kuma ka ambaci wani batun da za ku tattauna idan ka dawo.

  • Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) Ka yi amfani da shafuffuka na 206-208 na Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? wajen bayyana wa ɗalibi game da taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Ka ƙarfafa shi ya halarci taron.

RAYUWAR KIRISTA

  • Waƙa ta 5

  • Ku Gayyaci Kowa a Yankinku Zuwa Taron Tuna da Mutuwar Yesu!”: (minti 15) Tattaunawa. Ka bayyana yadda ikilisiyarku za ta rarraba takardar gayyatar a yankin baki ɗaya. Sa’ad da kake tattauna “Dabarun Da Za a Yi Amfani da Su,” ka saka bidiyon Tunawa da Mutuwar Yesu. Ka ƙarfafa ‘yan’uwa su saka hannu wajen rarraba takardar kuma su koma wurin waɗanda suka saurara. Ka sa a yi gwaji.

  • Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: ia babi na 9 sakin layi na 14-24, da tambayoyi don bimbini da ke shafi na 82 (minti 30)

  • Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)

  • Waƙa ta 39 da Addu’a