Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

29 ga Fabrairu–6 ga Maris

ESTHER 1-5

29 ga Fabrairu–6 ga Maris
  • Waƙa ta 86 da Addu’a

  • Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

  • Esther Ta Kāre Mutanen Allah”: (minti 10)

  • Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)

    • Es 2:15—Ta yaya Esther ta nuna halin filako da kuma kamun kai? (w06 3/1 30 sakin layi na 5)

    • Es 3:2-4—Mene ne wataƙila ya sa Mordekai ya ƙi rusuna wa Haman? (ia 131 sakin layi na 18)

    • Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?

    • Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?

  • Karatun Littafi Mai Tsarki: Es 1:1-15 (minti 4 ko ƙasa da hakan)

KA YI WA’AZI DA ƘWAZO

  • Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ku ba da ƙasidar nan Ka Saurari Allah. Ka yi wata tambaya ko kuma ka ambaci wani batun da za ku tattauna idan ka dawo.

  • Koma Ziyara: (minti 4 ko ƙasa da hakan) A nuna yadda ake gudanar da nazari sa’ad da aka koma ziyara wurin wani da ya karɓi ƙasidar nan Ka Saurari Allah, kuma ku tattauna shafuffuka na 2-3. Ka yi tambaya ko ka ambaci wani batun da za ku tattauna idan ka dawo.

  • Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) A nuna yadda ake gudanar da nazari ta wajen yin amfani da shafuffuka na 4-5 na ƙasidar nan Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada, idan maigidan ya karɓi Ka Saurari Allah a haɗuwa ta fari. (km 7/12 2-3 sakin layi na 4)

RAYUWAR KIRISTA

  • Waƙa ta 71

  • Bukatun ikilisiya: (minti 10)

  • Yaya Kuke Amfana Daga Sabon Tsarin Taronmu da Kuma Littafi don Taro?: (minti 5) Tattaunawa. Ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda suka amfana daga sabon tsarin taro. Ka ƙarfafa masu sauraro su riƙa yin shiri don su amfana.

  • Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: ia babi na 10 sakin layi na 1-11, da akwatin da ke shafi na 86 (minti 30)

  • Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)

  • Waƙa ta 113 da Addu’a