Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 58-62

‘Ku Yi Shelar Shekara ta Alherin’ Jehobah

‘Ku Yi Shelar Shekara ta Alherin’ Jehobah

“Shekara ta alherin” Jehobah ba shekara ta zahiri ba ce

61:1, 2

  • Lokaci ne da Jehobah ya ba wa mutane masu tawali’u su soma bauta masa

  • A ƙarni na farko, shekarar alherin ta soma a shekara ta 29 bayan haihuwar Yesu kuma ta ƙare a “ranar sakaiya” ta Jehobah, wato sa’ad da aka halaka Urushalima a shekara ta 70

  • A zamaninmu, shekarar ta soma sa’ad da aka naɗa Yesu sarki a sama a shekara ta 1914 kuma zai ƙare a lokacin ƙunci mai girma

Jehobah ya ba mu kyautar manyan “itatuwa na adalci”

61:3, 4

  • Itatuwa masu tsayi sosai ba sa kasancewa su kaɗai amma suna girma tare da wasu itatuwa a cikin daji

  • Jijiyoyinsu masu girma suna haɗuwa da juna kuma hakan na taimaka musu sa’ad da ake iska mai ƙarfi

  • Manyan itatuwa suna kāre ƙananan itatuwa daga zafin rana kuma ganyayensu da ke faɗiwa a ƙasa suna zama taki

Dukan ikilisiyoyi a faɗin duniya suna amfana daga kāriya da kuma taimakon da manyan “itatuwa na adalci” suke mana, wato shafaffun Kiristocin da suka rage a duniya