ISHAYA 63-66
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH |Sababbin Sammai da Sabuwar Duniya Za Su Sa Mu Murna Sosai
Jehobah yana da tabbaci sosai cewa zai cika alkawarin da ya yi na sabonta sammai da duniya a Ishaya sura 65, shi ya sa ya furta shi kamar ya riga ya cika.
Jehobah yana halittar sababbin sammai da sabuwar duniya, inda ba za a ƙara tunawa da al’amura na dā ba
65:17
Mene ne sababbin sammai?
-
Sabuwar gwamnati ce da za ta cire mugunta a duniya
-
An kafa ta a shekara ta 1914 sa’ad da Yesu ya soma sarauta a Mulkin Allah
Mece ce sabuwar duniya?
-
Mutane ne daga ƙabilai da harsuna da kuma ƙasashe dabam-dabam da suke goyon bayan Mulkin Allah
A wace hanya ce ba za a ƙara tuna da al’amura na dā ba?
-
Abubuwan da ke sa mu baƙin ciki ba za su riƙa faruwa ba
-
Mutane masu adalci za su riƙa jin daɗin rayuwa kowace rana