26 ga Fabrairu–4 ga Maris
MATTA 18-19
Waƙa ta 121 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ka Guji Sa Kanka da Kuma Wasu Yin Tuntuɓe”: (minti 10)
Mt 18:6, 7—Kada mu sa wasu tuntuɓe (nwtsty na nazari da kuma hotuna da bidiyo)
Mt 18:8, 9—Wajibi ne mu guji duk wani abin da zai sa mu tuntuɓe (nwtsty na nazari da kuma bayani a kan “Gehenna”)
Mt 18:10—Jehobah yana ganin mu idan muka sa wasu tuntuɓe (nwtsty na nazari; w11 1/1 24)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Mt 18:21, 22—Har sau nawa ne ya kamata mu gafarta wa ’yan’uwanmu? (nwtsty na nazari)
Mt 19:7—Me ya sa ake ba da “takardar kisan aure”? (nwtsty na nazari da kuma hotuna da bidiyo)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Mt 18:18-35
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi.
Komawa Ziyara ta Uku: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka zaɓi nassin da za ka yi amfani da shi kuma ba da ɗaya daga cikin littattafan da muke nazari da su.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) bhs 26 sakin layi na 18-20—Ka nuna yadda za a iya ratsa zuciyar ɗalibi.
RAYUWAR KIRISTA
Kada Ka Sa Wasu Tuntuɓe (2Ko 6:3): (minti 9) Ka saka bidiyon.
Za a Soma Rarraba Takardar Gayyata na Taron Tuna da Mutuwar Yesu a Ranar 3 ga Maris: (minti 6) Jawabin da aka ɗauko daga Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu na Fabrairu 2016, shafi na 8. A ba kowa kofi guda na takardar gayyatar kuma a tattauna abin da ke ciki. Ka gaya wa ’yan’uwa cewa a makon 19 ga Maris, 2018 ne za a ba da jawabi na musamman mai jigo “Shin, Waye ne Yesu Kristi?” Hakan zai sa ’yan’uwa su yi marmarin halartar taron. Ka bayyana yadda ikilisiyarku za ta rarraba takardar a yankin gabaki ɗaya.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 4 shafi na 46-49
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 133 da Addu’a