Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 12-13

Kwatancin Alkama da Zawan

Kwatancin Alkama da Zawan

Yesu ya yi amfani da kwatancin alkama da zawan wajen kwatanta yadda zai zaɓi shafaffun Kiristoci da suke kama da alkama daga cikin mutane da kuma lokacin da zai yi hakan. An soma hakan a shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu.

13:24

‘Wani mutum ya shuka iri mai-kyau cikin gonarsa’

  • Mai shukin: Yesu Kristi

  • Iri mai kyau da aka shuka: An shafe almajiran Yesu da ruhu mai tsarki

  • Gonar: Mutane

13:25

“Lokacin da mutane suna barci, maƙiyinsa ya zo, ya shuka zawan”

  • Maƙiyi: Shaiɗan

  • Da mutane suka yi barci: A lokacin da manzanni suka mutu

13:30

“Bar su duka biyu su yi girma tare har kaka”

  • Alkama: Shafaffun Kiristoci

  • Zawan: Kiristoci na ƙarya

‘Ku tattara zawan tukuna . . . ; kafin ku tattara alkama’

  • Bayi ko masu girbi: Mala’iku

  • Zawan da aka tattara: An ware Kiristoci na ƙarya daga shafaffun Kiristoci

  • Tattara su zuwa rumbu: An tattara shafaffun Kiristoci zuwa cikin ikilisiya

Idan aka soma girbin, ta yaya za a bambanta Kiristoci na gaskiya daga Kiristoci na ƙarya?

Wane darasi na koya daga wannan kwatancin?