12-18 ga Fabrairu
MATTA 14-15
Waƙa ta 93 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ya Ciyar da Dubbai Ta Hannun Mutane Ƙalila”: (minti 10)
Mt 14:16, 17—Mabiyan Yesu suna da burodi biyar da kuma kifi guda biyu kawai (w13 7/15 15 sakin layi na 2)
Mt 14:18, 19—Yesu ya yi amfani da almajiransa ya ciyar da dubban mutane (w13 7/15 15 sakin layi na 3)
Mt 14:20, 21—Mutane da yawa sun amfana daga mu’ujizar da Yesu ya yi (nwtsty na nazarin Mt 14:21; w13 7/15 15 sakin layi na 1)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Mt 15:7-9—Me ya sa ya kamata mu guji yin munafunci? (nwtsty na nazari)
Mt 15:26—Mene ne wataƙila Yesu yake nufi sa’ad da ya yi amfani da furucin nan ‘’ya’yan karnuka’? (nwtsty na nazari)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Mt 15:1-20
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi.
Bidiyon Komawa Ziyara ta Farko: (minti 5) Ka saka bidiyon kuma ku tattauna shi.
Jawabi: (minti 6 ko ƙasa da hakan) w15 9/15 16-17 sakin layi na 14-17—Jigo: Ka Bi Koyarwar Yesu Don Ka Karfafa Bangaskiyarka.
RAYUWAR KIRISTA
Ka Zama Abokin Jehobah—Yadda Za Ka Yi Abokai: (minti 7) Ka saka bidiyon. Bayan haka, ka gayyaci yara zuwa kan bagadi kuma ka yi musu waɗannan tambayoyin: Me ya sa yake da kyau ku yi abokantaka da waɗanda suke son Jehobah? Mene ne za ku iya koya daga wurinsu?
“Ka Girmama Mahaifinka da Mahaifiyarka”: (minti 8) Tattaunawa. Ka saka bidiyon nan Yadda Ya Kamata Ka Yi Magana da Iyayenka
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 4 sakin layi na 1-11
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 148 da Addu’a