Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

“Ka Girmama Mahaifinka da Mahaifiyarka”

“Ka Girmama Mahaifinka da Mahaifiyarka”

Sa’ad da Yesu yake duniya, ya nanata muhimmancin umurnin nan: “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.” (Fit 20:12; Mt 15:​4, Littafi Mai Tsarki) Hakika, Yesu bai ji kunyar faɗan haka ba domin ya yi wa iyayensa “biyayya” sa’ad da yake matashi. (Lu 2:51) Da ya girma, ya nemi wanda zai kula da mahaifiyarsa bayan ya mutu. ​—⁠Yoh 19:​26, 27.

A yau ma, Kiristoci matasa suna girmama iyayensu idan suna ma iyayensu biyayya kuma suna musu magana da daraja. Kuma umurnin da aka ba mu na girmama iyayenmu ba shi da iyaka. Ko da iyayenmu sun tsufa sosai, ya kamata mu ci gaba da girmama su ta wurin saurarar shawararsu. (Mis 23:22) Ƙari ga haka, muna daraja iyayenmu da suka tsufa ta wajen kula da su da kuma taimaka musu. (1Ti 5:8) Ko da mu matasa ne ko manya, ya kamata mu riƙa tattaunawa da kyau da iyayenmu domin hakan zai nuna cewa muna girmama su.

KU KALLI BIDIYON ZANEN ALLON NAN YADDA YA KAMATA KA YI MAGANA DA IYAYENKA SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Me ya sa zai iya yi maka wuya ka tattauna da iyayenka?

  • Ta yaya za ka girmama iyayenka sa’ad da kake magana da su?

  • Me ya sa yake da kyau ka tattauna da iyayenka? (Mis 15:⁠22)

    Idan kana tattaunawa da iyayenka, hakan zai sa ka yi nasara a rayuwa