RAYUWAR KIRISTA
Ku Rika Jira da Hakuri
Shekaru nawa ka yi kana jiran Mulkin Allah ya zo? Kana kan jira da haƙuri duk da matsalolin da kake fuskanta? (Ro 8:25) Wasu Kiristoci suna fuskantar ƙiyayya da kuma wulakanci. Wasu kuma an saka su a fursuna har ma ana barazanar cewa za a kashe su. Har ila, wasu suna fama da ciwo ko kuma tsufa.
Me zai taimaka mana mu riƙa jira da marmari duk da matsalolin da muke fama da su? Wajibi ne mu riƙa ƙarfafa bangaskiyarmu a kullum ta wurin karanta Kalmar Allah da kuma yin bimbini a kan abin da muka karanta. Zai dace mu mai da hankali a kan abin da muke begen sa. (2Ko 4:16-18; Ibr 12:2) Ƙari ga haka, ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah kuma mu roƙe shi ya taimaka mana da ruhunsa mai tsarki. (Lu 11:10, 13; Ibr 5:7) Idan muka yi hakan, Ubanmu mai ƙauna zai taimaka mana mu ‘jimre kowane abin da ya faru muna haƙuri da farin ciki.’—Kol 1:11.
KU KALLI BIDIYON NAN WAJIBI NE KU YI TSERE DA JIMIRI—KU KASANCE DA TABBACIN SAMUN LADAN, BAYAN HAKA, KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
-
Waɗanne abubuwa ne za mu iya fuskanta ba zato ba labari? (M. Wa 9:11)
-
Ta yaya addu’a za ta taimaka mana sa’ad da muke fuskantar matsaloli?
-
Idan ba ma iya yin abubuwan da muka saba yi a hidimarmu ga Jehobah, me ya sa zai dace mu mai da hankali a kan abin da za mu iya yi?
-
Me yake taimaka maka ka kasance da tabbaci cewa za ka sami ladan?