25 ga Fabrairu–3 ga Maris
ROMAWA 9-11
Waƙa ta 25 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Kwatancin Itacen Zaitun”: (minti 10)
Ro 11:16—Itacen zaitun yana wakiltar cikar abin da Allah yake so ya cim ma ta wurin alkawarin da ya yi da Ibrahim (w11 5/15 23 sakin layi na 13)
Ro 11:17, 20, 21—Dole ne Shafaffun da suke kama da reshe da aka yi masa aure da itacen zaitun su zama da bangaskiya a koyaushe (w11 5/15 24 sakin layi na 15)
Ro 11:25, 26—Za a “ceci” dukan adadin Kiristoci Shafaffu (w11 5/15 25 sakin layi na 19)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Ro 9:21-23—Me ya sa ya kamata mu ƙyale Jehobah ya ja-goranci tunaninmu kamar yadda mai ginin tukwane yake amfani da laka yadda yake so? (w13 6/15 25 sakin layi na 5)
Ro 10:2—Me ya sa ya dace mu tabbata cewa bautarmu ta yi daidai da gaskiyar Kalmar Allah? (mwbr19.02-HA an ɗauko daga it-1 1260 sakin layi na 2)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Ro 10:1-15 (th darasi na 10)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Bidiyon Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 5) Ku kalli bidiyon kuma ku tattauna shi.
Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. (th darasi na 6)
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5 ko ƙasa da hakan) Ka soma da bin abin da ke Yadda Za Mu YI Wa’azi na komawa ziyara ta biyu, sai ka soma nazari da littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? (th darasi na 9)
RAYUWAR KIRISTA
“Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Daina Nazari da Ɗaliban da Ba Sa Samun Ci gaba”: (minti 15) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) bhs babi na 4 sakin layi na 1-9 da ƙarin bayani na 12-13
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 36 da Addu’a