Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Daina Nazari da Daliban da Ba Sa Samun Ci gaba

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Daina Nazari da Daliban da Ba Sa Samun Ci gaba

MUHIMMANCINSA: Dole ne mutane su kira ga sunan Jehobah kafin su sami tsira. (Ro 10:​13, 14) Amma ba dukan mutane da suke nazari ne suke son su bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarsu ba. Mu riƙa amfani da lokacinmu don mu taimaka ma mutane da suke da niyar kyautata rayuwarsu yadda Allah yake so. Bayan mun yi nazari na wasu lokuta kuma muka gane cewa ɗalibin ba ya son ya canja halinsa, zai dace mu mai da hankalinmu ga mutanen da Jehobah yake jawo su gare shi da kuma ƙungiyarsa. (Yoh 6:44) Amma idan daga baya mutumin ya nuna cewa yana son ya samu “rai na har abada,” za mu yi farin cikin sake soma nazari da shi.​—A. M 13:48.

YADDA ZA MU YI HAKAN:

  • Ka yaba ma ɗalibin don yana son ya koyi gaskiya.​—1Ti 2:4

  • Ka nanata masa muhimmancin aikata abubuwan da yake koya.​—Lu 6:​46-49

  • Ka bayyana masa kwatancin Yesu game da mashuki, kuma ka gaya masa ya yi tunani a kan abin da yake hana shi aikata abin da yake koya.​—Mt 13:​18-23

  • Ka yi amfani da basira yayin da kake gaya masa cewa za ka dakatar da nazarin

  • Ka gaya masa za ka riƙa zuwa a wasu lokuta don ka ƙarfafa shi kuma za ku sake soma nazarin idan ya soma aikata abin da yake koya

KU KALLI BIDIYON, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Mene ne ka koya a wannan tattaunawa da ya nuna cewa ɗalibin ba ya aikata abin da yake koya?

  • Ta yaya mai shelan ya taimaka ma ɗalibin ya gane cewa yana bukatar ya riƙa aikata abubuwan da yake koya?

  • Ta yaya mai shelan ya nuna ma ɗalibin cewa zai sake soma nazarin idan ɗalibin ya soma aikata abin da yake koya?