Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ROMAWA 9-11

Kwatancin Itacen Zaitun

Kwatancin Itacen Zaitun

11:16-26

Mene ne sassa dabam-dabam na itacen zaitun take wakilta?

  • Itacen: cikar abin da Allah yake so ya cim ma ta wurin alkawarin da ya yi da Ibrahim

  • Jikin itacen: Yesu, wanda shi ne mutum mafi muhimmanci a zuriyar Ibrahim

  • Rassan: cikakken adadin Kiristoci Shafaffu

  • Rassan da aka “sassare”: Yahudawa da suka ƙi gaskata da Yesu

  • Rassan da aka haɗa da itacen: Kiristoci shafaffu da suka fito daga ƙasashe dabam-dabam

Kamar yadda aka annabta, zuriyar Ibrahim, wato Yesu da shafaffun Kiristoci 144,000 za su kawo albarka ga “dukan kabilun duniya.”​—Ro 11:12; Fa 22:18

Mene ne na koya game da yadda Jehobah ya cika alkawarin da ya yi game da zuriyar Ibrahim?