4-10 ga Janairu
2 Labarbaru 29-32
Waƙa ta 114 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Bauta ta Gaskiya Tana Bukatar Aiki Tuƙuru”: (minti 10)
2Lab 29:
10-17 —Hezekiya ya dawo da bauta ta gaskiya da himma 2Lab 30:
5, 6, 10-12 —Hezekiya ya gayyato dukan amintattu su haɗu don ibada 2Lab 32:
25, 26 —Hezekiya ya daina fahariya kuma ya kasance da sauƙin kai (w05 11/1 13 sakin layi na 20)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
2Lab 29:11
—Ta yaya Hezekiya ya kafa misali mai kyau wajen mai da hankali ga abubuwan da suka fi muhimmanci? (w13 11/15 17 sakin layi na 6-7) 2Lab 32:
7, 8 —Wane mataki mafi kyau ne za mu iya ɗauka don yin shiri game da munanan abubuwan da za mu fuskanta a nan gaba? (w13 11/15 20 sakin layi na 17) Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?
Karatun Littafi Mai Tsarki: 2Lab 31:
1-10 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Ka Shirya Gabatarwa na Wannan Watan: (minti 15) Tattaunawa. Ka saka bidiyon nan Gabatarwar Hasumiyar Tsaro na farko, bayan haka, ka tattauna wasu abubuwa a ciki. Ka nanata yadda mai shelar ta yi wata tambaya ko ta faɗi wani batun da za su tattauna sa’ad da ta dawo. Ka yi hakan ma da gabatarwar Hasumiyar Tsaro na biyu da kuma Albishiri Daga Allah! Ka yi magana a kan “Yadda Za a Yi Amfani da Albishiri Daga Allah! don Yin Nazari.” Ka ƙarfafa masu shela su rubuta nasu gabatarwa.
RAYUWAR KIRISTA
Waƙa ta 127
“Gatan Gina da Kuma Gyara Wuraren Ibadarmu”: (minti 15) Tattaunawa. Ka gayyaci waɗanda suka taɓa saka hannu a gina Majami’ar Mulki su faɗi irin farin cikin da suka yi. Ka ɗan gana da mai kula da tsabtace da gyara Majami’ar Mulki game da shirye-shiryen da aka yi a ikilisiyar don yin gyara da kuma shara.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: ia babi na 6 sakin layi na 1-14 (minti 30)
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 142 da Addu’a
Tunasarwa: Don Allah a saka wa masu sauraro sabuwar waƙar sau ɗaya, bayan haka, sai su rera waƙar tare.