KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Yadda Za a Yi Amfani da Albishiri Daga Allah! don Yin Nazari
-
Ka karanta tambayar da ke da lamba don ka taimaka wa maigidan ya mai da hankali ga darasin.
-
Ka karanta sakin layi na gaba.
-
Ka karanta nassosin da aka rubuta “karanta” kuma ka yi amfani da tambayoyi don taimaka wa maigidan ya ga yadda nassosin suka amsa tambaya da ke da lamba.
-
Idan akwai wani sakin layi a ƙarƙashin tambayar, ka maimaita batu na 2 da 3. Idan akwai wani bidiyo a dandalin jw.org da ya yi magana a kan tambayar, ka saka wa maigidan.
-
Don ka tabbata cewa maigidan ya fahimci batun, ka sa ya amsa tambayar da ke da lamba.