Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Gatan Gina da Kuma Gyara Wuraren Ibadarmu

Gatan Gina da Kuma Gyara Wuraren Ibadarmu

Gina haikali a zamanin Isra’ilawa ya bukaci aiki tuƙuru da kuma kuɗi mai yawa. Duk da haka, Isra’ilawa sun yi aikin da ƙwazo. (1Lab 29:2-9; 2Lab 6:7, 8) Gyare-gyaren da Isra’ilawa suka yi a haikalin bayan sun kammala ginin ya nuna ko suna da dangantaka mai kyau da Jehobah ko babu. (2Sa 22:3-6; 2Lab 28:24; 29:3) A yau, Kiristoci ma suna sa ƙwazo wajen gina da tsabtace da kuma gyara Majami’un Mulki da kuma Majami’un Manyan Taro. Yin irin waɗannan ayyukan ga Jehobah babban gata ne sosai kuma hakan ibada ce.Za 127:1; R. Yoh 7:15.

ZA MU IYA TAIMAKAWA TA WAJEN . . .

  • Tsabtace wuri bayan kowane taro. Idan ba za ka iya yin shara ba saboda yanayinka, ka kwashe duk wani datti da ke kewaye da kai.

  • Ba da kai a duk lokacin da ake share ko gyara Majami’ar Mulki. Idan mutane da yawa suka ba da kai wajen yin aikin, za a ji daɗi kuma aikin zai yi sauƙi.lv 92-93 sakin layi na 18.

  • Ba da gudummawar kuɗi. Ko da kuɗin da muke da shi ba yawa, Jehobah yana farin ciki da waɗanda suke bayarwa da zuciya ɗaya.Mk 12:41-44.

  • Ba da kai wajen gina da kuma gyara wuraren da muke ibada, idan zai yiwu. Ba sai ka iya gini ba ne za ka iya ba da kai.