Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

11-17 ga Janairu

2 Labarbaru 33-36

11-17 ga Janairu
  • Waƙa ta 35 da Addu’a

  • Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

  • Jehobah Yana Son Tuban Gaske”: (minti 10)

    • 2Lab 33:2-9, 12-16—Allah ya nuna wa Manassa jin ƙai domin ya tuba (w05 12/1 31 sakin layi na 4)

    • 2Lab 34:18, 30, 33—Karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini a kai zai taimaka mana sosai (w05 12/1 31 sakin layi na 9)

    • 2Lab 36:15-17—Bai kamata mu ɗauki tausayi da kuma haƙurin Jehobah da wasa ba (w05 12/1 31 sakin layi na 6)

  • Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)

    • 2Lab 33:11—Wane annabci ne ya cika sa’ad da aka kai Manassa bauta a Babila? (it-1-E 62 sakin layi na 2)

    • 2Lab 34:1-3—Wace ƙarfafa ce za mu iya samu daga misalin Josiah? (w05 12/1 31 sakin layi na 5)

    • Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?

    • Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?

  • Karatun Littafi Mai Tsarki: 2Lab 34:22-33 (minti 4 ko ƙasa da hakan)

KA YI WA’AZI DA ƘWAZO

  • Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ku gabatar da bangon Hasumiyar Tsaro ta kwanan nan. Ka yi wata tambaya ko kuma ka ambaci wani batun da za ku tattauna idan ka dawo.

  • Koma Ziyara: (minti 4 ko ƙasa da hakan) A nuna yadda ake koma ziyara wurin wani da ya karɓi Hasumiyar Tsaro ta kwanan nan. Ka yi wata tambaya ko kuma ka ambaci wani batun da za ku tattauna idan ka dawo.

  • Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) A nuna yadda ake gudanar da nazari. (bh shafi na 9-10 sakin layi na 6-7)

RAYUWAR KIRISTA