25- 31 ga Janairu
Ezra 6-10
Waƙa ta 10 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Jehobah Yana Son Masu Bauta da Zuciya Ɗaya”: (minti 10)
Ezr 7:10
—Ezra ya shirya zuciyarsa Ezr 7:
12-28 —Ezra ya yi shirin komawa Urushalima Ezr 8:
21-23 —Ezra ya tabbata Jehobah zai kāre bayinsa
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Ezr 9:
1, 2 —Me ya sa yin auratayya da “al’umman ƙasa” ba ƙaramin barazana ba ne? (w06 1/1 10 sakin layi na 3) Ezr 10:3
—Me ya sa aka kawar da dukan mata tare da ‘ya’yansu? (w06 1/1 10 sakin layi na 4) Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ezr 7:
18-28 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) A ba da Albishiri Daga Allah! kuma a tattauna darasi na 8, tambaya ta 1, sakin layi na 1. Ka yi tambaya ko ka ambaci wani batun da za ku tattauna idan ka dawo.
Koma Ziyara: (minti 4 ko ƙasa da hakan) A nuna yadda ake gudanar da nazari sa’ad da aka koma wurin wani da ya karɓi Albishiri Daga Allah! Ka tattauna darasi na 8, tambaya ta 1, sakin layi na 2. Ka yi tambaya ko ka ambaci wani batun da za ku tattauna idan ka dawo.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) A nuna yadda ake yin nazarin darasi na 8, tambaya ta 2 na Albishiri Daga Allah!
RAYUWAR KIRISTA
Waƙa ta 138
“Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi
—Yin Shiri don Ziyara ta Gaba”: (minti 7) Tattaunawa. A nuna darussan ta wajen saka bidiyon nan Yadda Za A Yi Wa’azi a Watan Janairu da ya nuna yadda mai shela yake yin wata tambaya ko ya ambata wani batun da za su tattauna sa’ad da ya koma wurin mutumin da ya ba Hasumiyar Tsaro da kuma Albishiri Daga Allah! Bukatun ikilisiya: (minti 8)
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: ia babi na 7 sakin layi na 15-27, da tambayoyi don bimbini da ke shafi na 66 (minti 30)
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 120 da Addu’a