LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Janairu 2017
Gabatarwa
Yadda za a iya ba da mujallar Hasumiyar Tsaro da kuma koyar da annabcin Littafi Mai Tsarki da ke faruwa a yau. Ka yi amfani da misalan nan don ka rubuta taka gabatarwar.
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Jehobah Yana Kula da Mutanensa
Kamar yadda maigida yake kula da bakinsa, haka ma Jehobah yake tanadar mana da abubuwa na ibada.
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Wani Sarki Za Ya Yi Mulki Cikin Adalci”
Sarki Yesu ya nada dattawa don su kula da tumakinsa. Za su taimaka wa tumakin Allah ta wajen yi musu ja-gora a ibadarsu.
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
An Albarkaci Hezekiya don Bangaskiyarsa
Assuriyawa sun so Yahudawa su ba da kai ba tare da sun yi yaki ba, amma Jehobah ya aiko da mala’ikansa don ya kāre Urushalima.
RAYUWAR KIRISTA
“Ya Jehobah, . . . a Gare Ka Na Dogara”
Ya kamata mu rika dogara ga Jehobah a kowane lokaci. Ta yaya Hezekiya ya nuna cewa yana dogara ga Allah?
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Jehobah Yana Ba da Karfi ga Masu-Kasala
Yadda gaggafa take tashi sama ta nuna yadda muke amfani da ikon Allah wajen cim ma ayyukanmu na ibada.
RAYUWAR KIRISTA
Ku Rika Addu’a a Madadin ‘Yan’uwan da Ake Tsananta Musu
Ta yaya za mu yi addu’a don mu taimaki Kiristocin da ake tsananta musu?
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Jehobah Allah Ne Mai Annabcin Gaskiya
Wajen shekara 200 kafin a halaka Babila, Jehobah ya yi amfani da Ishaya wajen annabta yadda za a yi hakan.