Gabatarwa
HASUMIYAR TSARO
Tambaya: Wasu mutane suna ɗauka cewa Littafi Mai Tsarki tsohon yayi ne. Mene ne ra’ayinka?
Nassi: 2Ti 3:
Abin da Za Ka Ce: Wannan talifin Hasumiyar Tsaro ya nuna bayanai masu kyau da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma yadda za mu iya jin daɗin karanta shi.
KU KOYAR DA GASKIYA
Tambaya: Shin ƙarshen duniya ya kusa?
Nassi: Mt 24:
Gaskiya: Annabcin Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa muna rayuwa ne a kwanaki na ƙarshe. Wannan albishiri ne domin abubuwa za su gyaru nan ba da daɗewa ba.
ALBISHIRI DAGA ALLAH!
Tambaya: Wasu sun yi imani cewa Allah ya halicci duniyar nan ne don ya san mutanen da suka cancanci yin rayuwa a sama. Mene ne ra’ayinka?
Abin da Za Ka Ce: Wannan ƙasidar tana ɗauke da bayanan da suka sa mutane da yawa su yi imani cewa Allah ya halicci duniyar nan don mutane su kasance a ciki har abada. Zan so in sake dawowa don mu tattauna tambaya ta farko da ke shafi na 10: “Me ya sa Allah ya halicci duniya?”
KA RUBUTA TAKA GABATARWA
Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.