Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Rika Addu’a a Madadin ‘Yan’uwan da Ake Tsananta Musu

Ku Rika Addu’a a Madadin ‘Yan’uwan da Ake Tsananta Musu

Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa Shaiɗan zai tsananta mana domin yana so mu daina bauta wa Jehobah. (Yoh 15:20; R. Yoh 12:17) Ta yaya za mu taimaka wa ’yan’uwanmu Kiristoci waɗanda ake tsananta musu a ƙasarsu? Za mu iya yin addu’a a madadinsu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Addu’ar mai-adalci tana da iko da yawa cikin aikinta.”Yaƙ 5:16.

Me za mu iya yin addu’a a kai? Za mu iya ce Jehobah ya taimaka wa ‘yan’uwanmu su kasance da gaba gaɗi. (Ish 41:10-13) Za mu kuma iya roƙan Jehobah ya sa mahukunta su fahimci muhimmancin bisharar da muke yi, domin mu riƙa ‘zama lafiya, rai kwance.’1Ti 2:1, 2, Littafi Mai Tsarki.

Sa’ad da ake tsananta wa Bulus da Bitrus a ƙarni na farko, Kiristocin sun ambata sunayen kowannensu a addu’a. (A. M. 12:5; Ro 15:30, 31) A yau, ko da ba mu san sunayen dukan waɗanda ake tsananta musu ba, shin za mu iya ambata ikilisiyar su da ƙasarsu da kuma yankinsu a addu’o’inmu?

Ka rubuta kasashen da ake tsananta wa Shaidun Jehobah da za ka so ka yi addu’a a madadinsu: