Ana ba da wata warƙa kusa da birnin Monrovia da ke ƙasar Laberiya

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Janairu 2018

Yadda Za Mu Yi Wa’azi

Yadda za mu tattauna da mutane game da ko shawarar Littafi Mai Tsarki tana da amfani har yanzu.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

“Mulkin Sama Ya Kusa”

Yohanna mai baftisma ya saukaka rayuwarsa don ya mai da hankali sosai ga yin nufin Allah. A zamaninmu, idan muka saukaka rayuwarmu, hakan zai taimaka mana mu yi kwazo a hidimar Allah.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Darussan da Muka Koya Daga Hudubar Yesu a kan Dutse

Mene ne ake nufi da mu yi mammarin karanta Kalmar Allah? Ta yaya za mu inganta yadda muke nazarin Kalmar Allah?

RAYUWAR KIRISTA

Ta Yaya Za Ka Yi Sulhu da Dan’uwanka Tukuna?

Mene ne Yesu ya koya mana game da dangantakarmu da ’yan’uwanmu da kuma ibadarmu ga Allah?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ku Saka Mulkin Allah Farko a Rayuwarku

A cikin abubuwan da muke addu’ar a kai, wanne ne ya kamata mu fi yin addu’a a kai?

RAYUWAR KIRISTA

Ku Daina Damuwa

A Hudubar da Yesu ya yi a kan Dutse, mene ne yake nufi sa’ad da ya ce wa mabiyansa su daina damuwa?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Yesu Ya Kaunaci Mutane

A lokacin da Yesu ya warkar da mutane, ya nuna yana da iko, amma mafi muhimmanci, ya kaunaci mutane kuma ya nuna musu tausayi.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Yesu Ya Karfafa Mutane Kuma Ya Sa Sun Sami Kwanciyar Hankali

A lokacin da muka dauki karkiyar Yesu sa’ad da muka yi baftisma, mun soma wani babban aiki ne mai wuya, amma idan muka ci gaba, za mu sami karfafa sosai.