1-7 ga Janairu
Matta 1-3
Waƙa ta 14 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Mulkin Sama Ya Kusa”: (minti 10)
[Ka saka bidiyon Gabatarwar Littafin Matta.]
Mt 3:1, 2—Yohanna mai baftisma ya yi shela cewa Sarkin Mulkin Allah ya kusan zuwa (nwtsty na nazari)
Mt 3:4—Yohanna mai baftisma ya sauƙaƙa rayuwarsa don ya mai da hankali sosai ga yin nufin Allah (nwtsty hotuna da bidiyo)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Mt 1:3—Me ya sa Matta ya ambata sunayen mata biyar a zuriyar Yesu maimakon sunayen mazaje kawai? (nwtsty na nazari)
Mt 3:11—Ta yaya muka san cewa baftisma ta ƙunshi nitsar da mutum cikin ruwa gabaki ɗaya? (nwtsty na nazari)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Mt 1:1-17
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Bidiyon Haɗuwa ta Fari: (minti 4) Ka nuna bidiyon kuma ku tattauna shi.
Komawa Ziyara ta Farko: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka duba shafi na 1.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) bhs 41-42 sakin layi na 6-7
RAYUWAR KIRISTA
Rahoton Hidima na Shekara-Shekara: (minti 15) Jawabin da dattijo zai bayar. Bayan ka karanta wasiƙar da ofishinmu suka aika game da rahoton hidima na shekara-shekara, ka gana da wasu masu shela da ka zaɓa da suke da labarai masu kyau na wa’azi a shekarar hidima da ta shige.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 2 sakin layi na 1-11
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 137 da Addu’a