15-21 ga Janairu
MATTA 6-7
Waƙa ta 21 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ku Saka Mulkin Allah Farko a Rayuwarku”: (minti 10)
Mt 6:10—A addu’ar misali, Mulkin Allah yana cikin abubuwan da Yesu ya fara ambatawa kuma hakan ya nuna muhimmancinsa (bhs 178 sakin layi na 12)
Mt 6:24—Ba za mu iya bauta wa Allah da “Dukiya” a lokaci ɗaya ba (nwtsty na nazari)
Mt 6:33—Jehobah zai biya bukatun dukan waɗanda suka saka Mulkinsa farko a rayuwarsu (nwtsty na nazari; w16.07 12 sakin layi na 18)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Mt 7:12—Ta yaya za mu bi umurnin da ke ayar nan sa’ad da muke shirya abin da za mu faɗa a wa’azi? (w14 5/15 14-15 sakin layi na 14-16)
Mt 7:28, 29—Mene ne taron jama’a suka yi sa’ad da suka ji koyarwar Yesu, kuma me ya sa suka yi hakan? (nwtsty na nazari)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Mt 6:1-18
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi. Ka amsa tambayar da ake yawan yi a yankinmu.
Komawa Ziyara Ta Farko: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi. Wanda ka fara yi ma wa’azi ba ya gida amma ka samu wani ɗan’uwansa a gidan.
Bidiyon Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 5) Ka saka bidiyon kuma ku tattauna shi.
RAYUWAR KIRISTA
“Ku Daina Damuwa”: (minti 15) Tattaunawa. Ka fara nuna bidiyon nan Darussa Daga Kwatancin da Yesu Ya Yi—Ku Dubi Tsuntsaye da Furannin Jeji.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 3 sakin layi na 1-7, da akwatin da ke shafi na 29
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 132 da Addu’a