22-28 ga Janairu
MATTA 8-9
Waƙa ta 17 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Yesu Ya Ƙaunaci Mutane”: (minti 10)
Mt 8:1-3—Yesu ya ji tausayin wani kuturu (nwtsty na nazarin Mt 8:3)
Mt 9:9-13—Yesu ya ƙaunaci mutanen da ake wulaƙanta su (nwtsty na nazarin Mt 9:10)
Mt 9:35-38—Ƙaunar da Yesu yake yi wa mutane ya sa ya yi wa’azi ko ma a lokacin da ya gaji, kuma ya yi addu’a don Allah ya aiko da ma’aikata da yawa (nwtsty na nazarin Mt 9:36)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Mt 8:8-10—Wane darasi ne za mu koya daga tattaunawar da Yesu ya yi da sojan nan? (w02 9/1 7 sakin layi na 16)
Mt 9:16, 17—Wane darasi ne Yesu yake son mutane su fahimta a kwatanci biyun nan da ya yi? (jy 70 sakin layi na 6)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Mt 8:1-17
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Komawa Ziyara ta Biju: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi. Bayan haka, ka gayyaci mutumin zuwa taro.
Komawa Ziyara ta Uku: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka zaɓi nassin da za ka yi amfani da shi, bayan haka, ka ba shi ɗaya daga cikin littattafan da muke amfani da su wajen nazari.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) bhs 47 sakin layi na 18-19
RAYUWAR KIRISTA
Hakika Allah Ya Mai da Shi Ubangiji da Kristi’—Sashe na 1, Taƙaitawa: (minti 15) Tattaunawa. Bayan ka karanta Matta 9:18-25 kuma kun ƙalli wannan bidiyon, sai ka yi waɗannan tambayoyin:
Ta yaya Yesu ya nuna cewa ya ƙaunar da matar da ke ciwo da kuma Yayirus?
Yaya wannan labarin ya shafi yadda kake ɗaukan annabcin da ke Littafi Mai Tsarki game abubuwan da za su faru idan Mulkin ya soma sarauta?
Ta yaya za mu yi koyi da yadda Yesu ya ƙaunaci mutane?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 3, sakin layi na 8-15, da akwatin da ke shafi na 30
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 95 da Addu’a