29 ga Janairu –4 ga Fabrairu
MATTA 10-11
Waƙa ta 4 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Yesu Ya Ƙarfafa Mutane Kuma Ya Sa Sun Sami Kwanciyar Hankali”: (minti 10)
Mt 10:29, 30—Tabbacin da Yesu ya ba mu cewa Jehobah yana ƙaunar kowanenmu yana ƙarfafa mu (nwtsty na nazari da kuma bidiyo)
Mt 11:28—Bauta wa Jehobah na ƙarfafa mu (nwtsty na nazari)
Mt 11:29, 30—Za mu sami ƙarfafa idan muka yi biyayya ga Kristi kuma muka bi umurninsa (nwtsty na nazarin Mt 11:29)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Mt 11:2, 3—Me ya sa Yohanna mai baftisma ya yi wannan tambayar? (jy 96 sakin layi na 2-3)
Mt 11:16-19—Mene ne ma’anar waɗannan ayoyin? (jy 98 sakin layi na 1-2)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Mt 11:1-19
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka dubi shafi na 1.
Komawa Ziyara ta Uku: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka zaɓi nassin da za ka karanta da kuma tambayar da za ku tattauna idan ka koma.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) bhs 45-46 sakin layi na 15-16—Ka gayyaci mutumin zuwa taro.
RAYUWAR KIRISTA
Ku Ƙarfafa ‘Masu Wahala da Kuma Masu Fama da Nauyin Kaya’: (minti 15) Ka saka bidiyon. Bayan haka, sai ka tattauna tambayoyi na gaba:
Waɗanne abubuwa ne suka faru a kwanan nan da ya sa mutane suke bukatar ƙarfafa?
Ta yaya Jehobah da Yesu suka yi amfani da ƙungiyarmu don su ƙarfafa mu?
Ta yaya Nassosi suke ƙarfafa mu?
Ta yaya dukanmu za mu ƙarfafa juna?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 3, sakin layi na 16-21
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 138 da Addu’a