8-14 ga Janairu
MATTA 4-5
Waƙa ta 82 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Darussan da Muka Koya Daga Huɗubar Yesu a kan Dutse”: (minti 10)
Mt 5:3—Za mu yi farin ciki idan muna marmarin karanta Kalmar Allah (nwtsty na nazari)
Mt 5:7—Za mu yi farin ciki idan muna nuna jin ƙai kuma muna jin tausayin mutane (nwtsty na nazari)
Mt 5:9—Za mu yi farin ciki idan muna zaman lafiya da mutane (nwtsty na nazari; w07 12/1 17)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Mt 4:9—Mene ne Shaiɗan ya so ya sa Yesu ya yi? (nwtsty na nazari)
Mt 4:23—Waɗanne ayyuka biyu masu muhimmanci ne Yesu ya yi? (nwtsty na nazari)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Mt 5:31-48
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ka duba shafi na 1.
Bidiyon Komawa Ziyara Ta Farko: (minti 5) Ka nuna bidiyon kuma ku tattauna shi.
Jawabi: (minti 6 ko ƙasa da hakan) w16.03 31-32—Jigo: Shaiɗan Ya Jarabci Yesu a Haikali Na Zahiri Ne, Ko Kuma a Wahayi?
RAYUWAR KIRISTA
Masu Albarka ne Waɗanda Aka Tsananta Musu Saboda Adalci: (minti 9) Ka saka bidiyon nan Iyalin Namgungs: An Saka Su a Fursuna don Imaninsu, kuma ka tattauna darussan da muka koya.
“Ta Yaya Za Ka Yi Sulhu da Ɗan’uwanka Tukuna?”: (minti 6) Tattaunawa. Ka nuna yadda mataki na ƙarshe a yanayoyi biyun ne ya fi dacewa.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 2, sakin layi na 12-21 da akwatin da ke shafi na 24
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 141 da Addu’a