Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ta Yaya Za Ka Yi Sulhu da Dan’uwanka Tukuna?

Ta Yaya Za Ka Yi Sulhu da Dan’uwanka Tukuna?

A ce kana Galili a zamanin Yesu kuma ka je Urushalima don ka yi Idin Bukkoki. Birnin ya cika da mutane da suka fito daga wurare dabam-dabam a duniya don idin. Kana son ka yi hadaya ga Jehobah. Ka dauƙi akuyarka kuma ka tafi inda za ka ba da hadaya. Da ka iso haikalin, sai ka ga cewa yana nan cike da mutanen da suka zo don su yi hadaya. Da lokacinka na yin hadayar ya yi, sai ka tuna cewa kana da matsala da wani ɗan’uwa da wataƙila shi ma ya zo idin ko kuma yana cikin birnin. Yesu ya faɗi abin da ya kamata ka yi. (Karanta Matta 5:24.) Ta yaya kai da mutumin za ku sasanta da juna kamar yadda Yesu ya faɗa? Ka saka maki a amsar da ka ga ya fi dacewa a shawarar da aka bayar a gaba.

ZAI DACE KA . . .

  • sasanta da mutumin idan ka tabbata cewa ka yi masa laifi

  • daidaita ra’ayinsa idan kana ganin kamar mutumin ma yana da laifi ko kuma ya cika ɗaukan abu da zafi

  • saurare shi yayin da yake faɗan abin da ke zuciyarsa ko da ba ka fahimci batun da kyau ba kuma ka roƙi gafara

ZAI DACE ƊAN’UWANKA YA . . .

  • gaya wa ’yan’uwa a ikilisiya irin kuskuren da ka yi masa don su taimaka masa

  • maka bakar magana kuma ya gaya maka duk wani kuskuren da ka yi masa kuma ya so ka amince da hakan

  • fahimci cewa kana da tawali’u da ƙarfin hali shi ya sa ka zo don ku sasanta kuma ya gafarta maka daga zuciyarsa

Ko da yake bautarmu a yau ba ta ƙunshi ba da hadayu ba, amma wane darasi ne Yesu yake so mu koya daga alaƙar da ke tsakanin zaman lafiya da ’yan’uwanmu da bautar da muke wa Allah?