Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kana ɗaukan matakai don ka cancanci yin baftisma?

RAYUWAR KIRISTA

Ka Zaɓi Bauta wa Jehobah

Ka Zaɓi Bauta wa Jehobah

Idan ba ka yi baftisma ba ko kuma kai ɗalibi ne da ke nazarin Littafi Mai Tsarki, shin za ka so ka yi baftisma? Me ya sa ya kamata ka yi baftisma? Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma, hakan zai sa ka kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. (Za 91:1) Kuma yin hakan zai sa ka sami ceto. (1Bi 3:21) Waɗanne matakai ne za ka ɗauka don ka cancanci yin baftisma?

Ka yi nazari don ka gamsar da kanka cewa wannan ce gaskiya. Idan kana da tambayoyi, ka yi bincike da kanka don ka san amsarsu. (Ro 12:2) Ka bincika kanka don ka ga inda kake bukatar gyara kuma ka yi hakan saboda ƙaunar da kake yi wa Jehobah. (K. Ma 27:11; Afi 4:​23, 24) Ka riƙa neman taimakonsa. Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai yi amfani da ruhunsa mai tsarki don ya ƙarfafa da kuma taimaka maka. (1Bi 5:​10, 11) Ba za ka yi da-na-sanin yin hakan ba, domin bauta wa Jehobah ita ce abu mafi muhimmanci a rayuwa!​—Za 16:11.

KU KALLI BIDIYON NAN MATAKAN DA ZA KA ƊAUKA KAFIN YIN BAFTISMA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne matsaloli ne wasu suka magance don su iya yin baftisma?

  • Ta yaya za ka iya sa bangaskiyarka ta yi ƙarfi don ka iya yi wa Jehobah alkawarin bauta masa?

  • Mene ne ya sa wasu suka ɗauki matakin yin baftisma?

  • Waɗanne albarku ne waɗanda suka zaɓi su bauta wa Jehobah za su samu?

  • Mene ne yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma suke nufi?