Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Kāre Aurenku

Ku Kāre Aurenku

Jehobah yana ɗaukan alkawari da ma’aurata suka yi wa juna da muhimmanci kuma ya ce dole ne su manne wa juna. (Mt 19:​5, 6) A ƙungiyar Jehobah, akwai ma’aurata da yawa da suke kafa mana misali mai kyau. Duk da haka, ba ma’aurata da ba sa fuskantar matsala. Amma kada mu yarda da ra’ayin mutanen duniya cewa rabuwa ko kashe aure ne zai magance matsalolin. Ta yaya Kiristoci ma’aurata za su kāre aurensu?

Bari mu bincika hanyoyi guda biyar.

  1. Ku guji kwarkwasa da nishaɗi da ke ɗauke da lalata domin yin hakan zai ɓata aurenku.​—Mt 5:28; 2Bi 2:14.

  2. Ku ƙarfafa dangantakarku da Allah kuma ku ƙara ƙwazo wajen nuna cewa kuna so ku faranta masa rai a aurenku.​—Za 97:10.

  3. Ku ci gaba da nuna sabon hali kuma ku riƙa yi wa juna alheri domin ku ji daɗin aurenku.​—Kol 3:​8-10, 12-14.

  4. Ku riƙa tattauna abubuwan da suke damin ku a kullum kuma ku yi hakan da daraja.​—Kol 4:6.

  5. Namiji ya ba matarsa hakkinta na aure, matar ma ta yi hakan.​—1Ko 7:​3, 4; 10:24.

Idan Kiristoci suka daraja aurensu, hakan zai nuna cewa suna daraja Jehobah wanda ya kafa aure.

KU KALLI BIDIYON NAN WAJIBI NE KU YI TSERE DA JIMIRI​—KU BI DOKOKIN GASAR, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ko da yake ma’aurata sukan soma aure da farin ciki, waɗanne matsaloli ne za su iya fuskanta?

  • Ta yaya ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka ma waɗanda suke ganin ba sa jin daɗin aurensu?

  • Ku bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don ku yi farin ciki a aurenku

    Waɗanne dokoki ne Jehobah ya ba wa ma’aurata?

  • Me ya zama dole ma’aurata su yi idan suna so su yi farin ciki a aurensu?