Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Taron Yanki Yana Ba Mu Damar Nuna Ƙauna

Taron Yanki Yana Ba Mu Damar Nuna Ƙauna

Me ya sa muke jin daɗin taron yankin da muke yi a kowace shekara? Kamar yadda yake a zamanin Isra’ilawa, taron yankinmu yana ba mu damar bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwanmu da yawa. Muna jin daɗin dukan bayanan da muke samu da suke sa mu ci gaba da kasance kusa da Jehobah. Ban da haka ma, muna jin daɗin yin tarayya da ’yan’uwa da abokan arziki. Shi ya sa mukan halarci taron na kwanaki uku don mu nuna godiyarmu.

Idan muka sami damar taruwa, kada mu mai da hankali ga abin da zai amfane mu kawai, amma mu nemi zarafi don mu nuna ma ’yan’uwanmu ƙauna. (Ga 6:10; Ibr 10:​24, 25) Idan muka keɓe wurin zama da muke bukata kawai kuma ba mu tare hanya da ’yan’uwanmu suke bi ba, hakan zai nuna cewa muna mai da hankali ga abin da zai amfani ’yan’uwanmu. (Fib 2:​3, 4) A taron yanki, muna samun damar yin sabbin abokai. Kafin ko kuma bayan an gama taro da kuma lokacin cin abinci da rana, za mu iya amfani da waɗannan zarafin mu nemi sabbin abokai. (2Ko 6:13) Idan mun yi abokantaka a lokacin taron yanki, abokantakarmu za ta iya kasance har abada! Abin da ya fi muhimmanci kuma shi ne idan mutane sun ga yadda muke nuna wa juna ƙauna, hakan zai iya sa su ma su soma bauta wa Jehobah.​—Yoh 13:35.

KU KALLI BIDIYON NAN TARON ƘASA DA ƘASA NA “ƘAUNA BA TA ƘAREWA”! SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya aka nuna ƙauna ga ’yan’uwa da suka halarci taron ƙasa da ƙasa na 2019?

  • Me ya sa ƙauna da haɗin kai da ke tsakanin bayin Allah suke da ban sha’awa?

  • Wace irin ƙauna ta Kirista ce membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu suka tattauna?

  • Ta yaya kai ma za ka nuna ƙauna a taron yanki?

    Ta yaya ’yan’uwanmu suka ci gaba da nuna ƙauna ba fasawa a ƙasar Jamus da Koriya ta Kudu?

  • Me ya kamata mu kudiri aniyar yi?