RAYUWAR KIRISTA
Za Ka Iya Yin Hidimar Majagaba na Ɗan Lokaci a Watan Maris da Afrilu?
Za ka so ka faɗaɗa hidimarka a lokacin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu? (2Ko 5:14, 15) Waɗanda za su yi hidima na ɗan lokaci a watan Maris da Afrilu za su iya ba da awa 30 ko 50. Idan kana so ka yi wannan hidimar, ka cika fam ɗin kuma ka ba Kwamitin Hidima na Ikilisiyarku. A kowane wata, ana sanar da sunayen ’yan’uwa da suka ba da kai su yi hidima na ɗan lokaci ga ikilisiya. Hakan zai sa ’yan’uwa a ikilisiya su taimaka musu don su iya ba da awoyi da ake bukata a gare su. Bari dukanmu mu yi amfani da damar da muka samu don mu kyautata yadda muke wa’azi kuma mu ƙarfafa juna.—1Ta 5:11.