Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Iyaye, Ku Koyar da Yaranku Sosai

Iyaye, Ku Koyar da Yaranku Sosai

Muna rayuwa ne a duniyar da mutane suke ƙoƙarin mai da mugunta kamar nagarta, nagarta kuma kamar mugunta. (Ish 5:20) Abin baƙin ciki shi ne, mutane suna yin abubuwan da Jehobah ba ya so kamar lalata tsakanin jinsi ɗaya. Tsaran yaranmu a makaranta ko wasu za su iya ƙoƙari su ruɗe su su yi abubuwa marasa kyau. Ta yaya za ku taimaka wa yaranku don kada su faɗa a irin waɗannan tarkunan?

Ku koya wa yaranku ƙa’idodin Jehobah. (L.Fi 18:3) A hankali kuma bisa shekarunsu, ku koya musu abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da jima’i da kuma lalata. (M.Sh 6:7) Ku tambayi kanku: ‘Shin mun koyar da yaranmu yadda za su nuna ƙauna a hanyar da ta dace? Mun koyar da su muhimmancin saka tufafi da suka dace kuma kada su yarda mutane su gani ko taɓa wasu gaɓaɓuwan jikinsu? Yaranmu sun san abin da za su yi idan wani yana so ya nuna musu batsa ko yana so ya sa su yi wani abu da Jehobah ba ya so?’ Idan suka san waɗannan abubuwan tun da wuri, za su iya guje wa matsaloli da yawa. (K. Ma 27:12; M. Wa 7:12) Idan kuna koyar da yaranku, kuna nuna cewa kuna daraja kyautar yara da Jehobah ya ba ku.​—Za 127:3.

KU KALLI BIDIYON NAN KU GINA GIDAN DA ZAI DAWWAMA​—KU KIYAYE YARANKU DAGA “ABIN DA KE MUGU,” SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Me ya sa wasu ba sa so su koyar da yaransu game da jima’i?

  • Me ya sa ya zama dole iyaye su yi wa yaransu “horo da gargaɗi ta hanyar Ubangiji”?​—Afi 6:4

  • Ilimi yakan kāre mu

    Me ƙungiyar Jehobah ta tanadar da zai taimaka wa iyaye su koya wa yaransu game da jima’i?​—w19.05 12, akwatin

  • Me ya sa yake da muhimmanci iyaye su riƙa tattaunawa da yaransu a kullum kafin su fuskanci matsaloli?