RAYUWAR KIRISTA
Darussa da Muka Koya Daga Rayuwar Sama’ila
Sama’ila ya kasance da aminci ga Jehobah. Sa’ad da yake yaro, bai yi mugayen ayyuka kamar yaran Eli wato, Hophni da Phinehas ba. (1Sam 2:22-26) Sama’ila ya ci gaba da girma, kuma Jehobah ya kasance tare da shi. (1Sam 3:19) Sa’ad da ya tsufa ma, ya ci gaba da kasancewa da aminci ga Jehobah duk da cewa yaransa ba su bi halinsa ba.—1Sam 8:1-5.
Mene ne labarin Sama’ila ya koya mana? Idan kai matashi ne, zai dace ka kasance da tabbaci cewa Jehobah ya fahimci ƙalubale da kake fuskanta da kuma yadda kake ji. Zai iya taimaka maka ka kasance da karfin zuciya. (Ish 41:10, 13) Iyaye da ɗansu ko ’yarsu ta daina bauta wa Jehobah kuma fa? Ku ma za ku iya yin koyi da yadda Sama’ila bai tilasta wa yaransa su ci gaba da bin ƙa’idodin Jehobah ba. Amma ya bar kome a hannun Jehobah, sa’an nan ya ci gaba da riƙe amincinsa da kuma faranta ran Jehobah. Misali mai kyau da kuka kafa zai iya sa ɗanku ko ’yarku ta komo ga Jehobah.
KU KALLI BIDIYON NAN KU YI KOYI DA SU—SAMA’ILA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Ta yaya Sama’ila ya nuna ƙarfin zuciya sa’ad da yake yaro?
-
Ta yaya Danny ya nuna ƙarfin zuciya?
-
Ta yaya Sama’ila ya kafa misali mai kyau sa’ad da ya tsufa?
-
Ta yaya iyayen Danny suka kafa misali mai kyau?