Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Jehobah Zai Nuna Muku Kauna Marar Canjawa

Jehobah Zai Nuna Muku Kauna Marar Canjawa

Jehobah yana ɗaukanku da daraja sosai. (Ish 43:4) Shi ya taimaka muku ku bauta masa kuma ku kasance a ƙungiyarsa. Yanzu ku bayinsa ne domin kun yi alkawarin bauta masa kuma kun yi baftisma. Zai kula da ku sosai ko da kuna cikin mawuyacin yanayi. Zai ci gaba da nuna muku ƙauna sosai ta wurin ƙungiyarsa.—Za 25:10.

Wata hanya da za mu iya nuna godiya don ƙaunar Jehobah ita ce ta yin la’akari da yadda ƙungiyarsa ta taimaka sa’ad da bala’o’i suka auku a kwanan nan.

KU KALLI BIDIYON NAN RAHOTON KWAMITIN MASU TSARA AYYUKA NA 2019, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya Kwamiti Masu Tsara Ayyuka suke taimaka wa ofisoshinmu a faɗin duniya su yi shiri don bala’i da zai iya aukuwa?

  • Ta yaya ƙungiyar Jehobah ta taimaka wa ’yan’uwa a Indonesiya da kuma Nijeriya?

  • Mene ne ya burge ka game da matakai da ƙungiyar Jehobah ta ɗauka a kan annobar Korona?