DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Da Farko Saul Mai Tawali’u Ne Kuma Ya San Kasawarsa
Saul ya nuna sauƙin kai kuma ya yi jinkirin a naɗa shi sarki (1Sam 9:21; 10:20-22; w20.08 10 sakin layi na 11)
Saul bai ɗau mataki da gaggawa ba sa’ad da aka yi masa baƙar magana (1Sam 10:27; 11:12, 13; w14 3/15 9 sakin layi na 8)
Saul ya bi ja-gorancin ruhu mai tsarki (1Sam 11:5-7; w95-E 12/15 10 sakin layi na 1)
Tawali’u zai taimaka mana mu ga ayyukan da aka ba mu a ƙungiyar Jehobah da baiwar mu a matsayin kyauta daga wurin Jehobah. (Ro 12:3, 16; 1Ko 4:7) Ƙari ga haka, idan mu masu tawali’u ne, za mu ci gaba da dogara ga Jehobah don ya yi mana ja-goranci.