Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Matasa, Ku Rika Gaya wa Iyayenku Abin da Ke Damunku

Matasa, Ku Rika Gaya wa Iyayenku Abin da Ke Damunku

Me ya sa zai dace ku riƙa gaya wa iyayenku abin da ke zuciyarku? (K. Ma 23:26) Domin Jehobah ya ba su hakin kula da ku da kuma taimaka muku. (Za 127:3, 4) Zai yi musu wuya su taimaka muku idan kuka ɓoye abin da ke damunku. Kuma ba za ku san abubuwa game da rayuwa da suka sani ba. Laifi ne ku bar wasu abubuwa a zuciyarku? Ba lallai ba, muddin ba ku ruɗi iyayenku ba.—K. Ma 3:32.

Ta yaya za ku yi magana da iyayenku? Ku zaɓi lokacin da ya dace. Idan hakan zai yi wuya, za ku iya rubuta wa mamarku ko babanku wasiƙa don ku bayyana yadda kuke ji. Idan kuma iyayenku suna so su tattauna wani batu da ba za ku so ku tattauna da su ba fa? Ku tuna cewa suna so su taimaka muku ne. Iyayenku abokanku ne ba maƙiyanku ba. Idan kun yi ƙoƙarin tattaunawa da iyayenku, za ku amfana har abada!—K. Ma 4:10-12.

KU KALLI BIDIYON NAN RAYUWAR MATASA—TA YAYA ZAN YI WA IYAYENA MAGANA? SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Mene ne Esther da Partik suka fahimta game da kansu?

  • Mene ne za ka iya koya daga misalin Yesu?

  • Ta yaya iyayenka suka nuna maka cewa sun damu da kai?

  • Iyayenka suna so ka yi nasara

    Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka maka ka iya yi wa iyayenka magana?