Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ka Ƙarfafa Bangaskiyarka ga Kalmar Allah

Ka Ƙarfafa Bangaskiyarka ga Kalmar Allah

Littafi Mai Tsarki zai iya canja rayuwarmu. (Ibr 4:12) Amma kafin mu amfana daga shawarwarin da ke ciki, muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa “kalmar Allah” ne. (1Ta 2:13) Ta yaya za ka ƙarfafa bangaskiyarka ga Kalmar Allah?

Ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. Yayin da kake karantawa, ka nemi abin da ya nuna cewa Jehobah ne mawallafinsa. Alal misali, ka bincika shawarwarin da ke littafin Karin Magana don ka ga yadda za ka yi amfani da su a rayuwarka.​—K. Ma 13:20; 14:30.

Ka tsara yadda za ka riƙa nazari. Ka yi ƙoƙari ka san abubuwan da za su tabbatar maka cewa Littafi Mai Tsarki daga Allah ne. A Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah, ka duba ƙarƙashin jigon nan “Littafi Mai Tsarki” sai ka duba “Allah Ne Ya Hure.” Za ka kuma iya ƙarfafa bangaskiyarka cewa ba a canja abin da ke Littafi Mai Tsarki ba ta wurin bincika abin da ke Hasumiyar Tsaro Na 4 2016.

KU KALLI BIDIYON NAN ABIN DA YA SA MUKA GASKATA . . . LITTAFI MAI TSARKI KALMAR ALLAH CE, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya abin da aka gano a bangon haikali da ke Karnak a Masar, ya nuna cewa abin da ke Kalmar Allah gaskiya ne?

  • Ta yaya muka sani cewa abin da ke Littafi Mai Tsarki bai canja ba?

  • Ta yaya yadda aka kāre Littafi Mai Tsarki har wa yau ya tabbatar maka cewa Kalmar Allah ne? ​—Karanta Ishaya 40:8