20-26 ga Fabrairu
1 TARIHI 17-19
Waƙa ta 110 da Adduꞌa
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ka Ci-gaba da Farin Ciki a Duk Yanayi da Ka Sami Kanka”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
1Tar 17:16-18—Kamar Dauda, wane tabbaci ne za mu iya kasancewa da shi? (w20.02 12, akwati)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da waꞌazi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) 1Tar 18:1-17 (th darasi na 2)
KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 3) Ka soma da batun da ke yadda za mu yi waꞌazi. Ka gabatar kuma ka tattauna (amma kar ka kunna) bidiyon nan Su Wane ne Shaidun Jehobah? (th darasi na 17)
Komawa Ziyara: (minti 4) Ka soma da batun da ke yadda za mu yi waꞌazi. Ka ba da ɗaya daga cikin littattafan da ke Kayan Aiki don Koyarwa. (th darasi na 3)
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5) lff darasi na 09 batu na 4 (th darasi na 9)
RAYUWAR KIRISTA
Rahoton Hidima na Shekara-Shekara: (minti 15) Tattaunawa. Bayan ka karanta wasiƙar da aka aiko daga ofishinmu game da rahoton hidima na shekara-shekara, ka gaya wa masu sauraro su ambata wasu fannoni masu kyau da ke Rahoton Hidima na Shekara-shekara na Shaidun Jehobah na 2022. Ka gana da wasu masu shela da ka zaɓa da suke da labarai masu kyau game da waꞌazin da suka yi a shekarar hidima da ta shige.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lff darasi na 38 batu na 1-4
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 141 da Adduꞌa